Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Bitrus 1:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Maganar Ubangiji kuwa dawwamammiya ce,” Ita ce maganar bishara da aka yi muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Bitrus 1:25
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hakika ciyawa takan bushe, furanni kuwa su yi yaushi, Amma maganar Allah ba za ta taɓa faɗuwa ba!”


Hakika ina gaya muku, kafin sararin sama da ƙasa su shuɗe, ko wasali ko ɗigo na Attaura ba za su shuɗe ba, sai an cika dukan kome.


Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji, A kafe take a Sama.


Shi da yake tun fil'azal yake nan, wanda muka ji, muka gani da idonmu, muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, a game da Kalmar Rai,


Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku.


Amma kai, ya Ubangiji, sarki ne kai har abada, Dukan zamanai masu zuwa za su tuna da kai.


Duk da haka, zai fi sauƙi sararin sama da ƙasa su shuɗe, da ɗigo ɗaya na Attaura ya gushe.”


Ya kuwa zo ya yi muku albishirin salama, ku da kuke nesa, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.


Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.


Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.


Su za su ɓace duka, amma kai za ka dawwama, Za su ƙare kamar yadda tufafi suke ƙarewa, Za ka sāke su kamar tufafi, za su kuwa ɓace.


to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.


Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,


Gama sāke haifuwarku aka yi, ba ta iri mai lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, wato, ta Maganar Allah rayayyiya dawwamammiya.


An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani.


ya kuwa bayyana maganarsa a lokacin da ya ƙayyade, ta wa'azin da shi Allah Mai Cetonmu ya amince mini in yi, bisa ga umarninsa,


Ko da yake ni ne mafi ƙanƙantar tsarkaka duka, ni aka ba wannan alheri in yi wa al'ummai bishara a kan yalwar Almasihu marar ƙididdiguwa,


Don na ƙudura a raina, sa'ad da nake zaune da ku, ba zan so sanin kome ba, sai dai Yesu Almasihu, shi ma kuwa gicciyeyye.


Murya ta yi kira ta ce, “Ka yi shela!” Na yi tambaya na ce, “Shelar me zan yi?” “Ka yi shela, cewa dukan 'yan adam kamar ciyawa suke, Ba su fi furannin jeji tsawon rai ba.


har suka ɗanɗana daɗin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa,


Sa'an nan na ga wani mala'ika yana kaɗawa a tsakiyar sararin sama, yana tafe da madawwamiyar bishara, domin ya sanar da ita ga mazaunan duniya, wato, ga kowace al'umma, da kabila, da harshe, da jama'a.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ