1 Bitrus 1:17 - Littafi Mai Tsarki17 Da yake kuna kiransa Uba a wajen addu'a, shi da yake yi wa kowa shari'a gwargwadon aikinsa, ba zaɓe, sai ku ƙarasa lokacin baƙuncinku, kuna tsoronsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202017 Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ku dubi fa irin himmar da baƙin cikin nan, da Allah yake so ya sa a zukatanku, da irin ɗokin da kuka yi na gyara al'amuranku, da irin haushin da kuka ji, da irin tsoron da kuka ji, da irin begen da kuka yi, da irin himmar da kuka yi, da kuma irin niyyarku ta horo. A game da wannan sha'ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.