16 Domin a rubuce yake cewa, “Sai ku zama tsarkaka domin ni mai tsarki ne.”
16 gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
Ni ne Ubangiji Allahnku, domin haka dole ku tsarkake kanku, ku tsarkaka, gama ni mai tsarki ne.
ya faɗa wa dukan taron jama'ar Isra'ila cewa, “Ku zama tsarkakakku, gama ni Ubangiji Allahnku mai tsarki ne.
Sai ku kiyaye kanku da tsarki, gama ni ne Ubangiji Allahnku.
Zai yiwu a ce mutum biyu za su yi tafiya tare, Amma su rasa shirya magana?
Ni ne Ubangiji wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar domin in zama Allahnku. Sai ku zama tsarkakakku, gama ni mai tsarki ne.
Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.