1 Bitrus 1:12 - Littafi Mai Tsarki12 An dai bayyana musu, cewa ba kansu suke bauta wa ba, ku suke bauta wa, a game da abubuwan da masu yi muku bishara, ta ikon Ruhu Mai Tsarki, wanda aka aiko daga sama suka samar da ku a yanzu. Su ne kuwa abubuwan da mala'iku suke ɗokin gani. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202012 Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai na ji wani mai tsarki yana magana, wani kuma mai tsarki ya tambayi wancan mai tsarki da ya yi magana, ya ce, “Sai yaushe za a tsai da abubuwan da suke a wahayin nan, wato hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum, da zunubin da yake lalatarwa, da ba da wuri mai tsarki ga rundunar mutane don a tattake?”