Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 3:6 - Sabon Rai Don Kowa 2020

6 “Na daddatse al’ummai; an kuma rurrushe kagararsu. Na bar titunansu ba kowa, ba mai ratsawa a ciki. An ragargaza biranensu; ba wanda za a bari, babu ko ɗaya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

6 Ubangiji ya ce, “Na datse al'umman duniya, Hasumiyansu sun lalace. Na kuma lalatar da hanyoyinsu, Ba mai tafiya a kansu. An mai da biranensu kufai, Ba mutumin da yake zaune ciki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 3:6
19 Iomraidhean Croise  

Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.


Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance!


Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,


Wane mutum ne yana da isashiyar hikimar fahimtar wannan? Wa Ubangiji ya umarta da zai iya yin bayani? Me ya sa aka lalace ƙasar ta zama kufai kamar hamada da ba wanda zai iya ratsa ta?


Zan mai da biranenku kango, in lalace wuraren tsarkinku, ba zan kuma shaƙi ƙanshi hadayunku ba.


Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku, Ya ku mutanen Keretawa; maganar Ubangiji tana gāba da ke, Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa. “Zan hallaka ki kuma babu abin da zai rage.”


‘Na warwatsar da su da guguwa a cikin dukan ƙasashe, inda suka zama baƙi. Aka bar ƙasar ta zama kango bayansu, da har ba mai shiga ko fita. Haka suka sa ƙasan nan mai daɗi ta zama kango.’ ”


Ga shi, an bar muku gidanku a yashe.


Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.


To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.


Ku tuna yadda na rarraba wa kabilanku ƙasashen nan su zama naku na gādo, dukan ƙasashen da suka rage, ƙasashen da na ci da yaƙi, tsakanin Urdun da Bahar Rum a yamma.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan