Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
Ko da yake mayaƙan Arameyawa sun zo da mutane kaɗan kawai, Ubangiji ya sa suka ci nasara a kan sojojin Yahuda mafi yawa, don mutanen Yahuda sun rabu da Ubangiji Allah na kakanninsu, aka kuma hukunta Yowash.
Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.
Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,
Zan yi umarni, in ji Ubangiji, zan kuma komo da su wannan birni. Za su kuwa yi yaƙi da ita, su ƙwace ta su kuma ƙone ta. Zan kuma mai da garuruwan Yahuda kufai don kada wani ya zauna a can.”
Ka kuma faɗa wa Yehohiyakim sarkin Yahuda cewa, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, ka ƙone wancan littafin ka kuma ce, “Don me ka rubuta a cikinsa, cewa lalle sarkin Babilon zai zo ya hallaka wannan ƙasa, zai kashe mutum duk da dabba?”
“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa fushina da hasalata za su kwarara a wannan wuri, a kan mutum da dabba, a kan itatuwan fili da a kan amfanin gona, za su yi ta kuna, ba kuwa za a kashe ba.
Ubangiji ya yi abin da ya shirya; ya cika maganarsa, wadda ya umarta tun daɗewa. Ya jefar da ke ba tausayi, ya bari maƙiya sun yi nasara da ke, ya ɗaukaka ƙahon maƙiyanki.