Yunana 2:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki9 Amma ni zan raira yabbai gare ka, Zan miƙa maka sadaka, Zan cika wa'adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.” Faic an caibideil |
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.