Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yunana 1:7 - Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Matuƙan jirgin suka ce wa juna, “Ku zo, mu jefa ƙuri’a mu ga wa ke da alhakin wannan masifa.” Sai suka jefa ƙuri’a, ƙuri’ar kuwa ta fāɗa a kan Yunana.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

7 Matuƙan jirgin kuwa suka ce wa junansu, “To, bari mu jefa kuri'a mu gani ko alhakin wane ne ya jawo mana wannan bala'i da muke ciki.” Sai suka jefa kuri'a, kuri'ar kuwa ta fāɗa a kan Yunusa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yunana 1:7
18 Iomraidhean Croise  

A shekara ta goma sha biyu ta Sarki Zerzes, a wata na farko, watan Nisan, sai suka jefa fur (wato, ƙuri’a) a gaban Haman don a zaɓi rana da watan da zai dace da ƙulle-ƙullen. Sai ƙuri’a ta fāɗa a kan wata na goma sha biyu, wato, watan Adar.


Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.


Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.


Akan jefa ƙuri’a a kan cinya, amma kowace shawara mai kyau daga Ubangiji ne.


“Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku.


Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.


ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa.


Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.


Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka tashi! Me kake yi kwance rubda ciki?


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan