Yunana 1:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 Dukan matuƙan jirgin suka tsorata, kowannensu kuma ya yi kuka ga allahnsa, suka kuma jefar da kayan jirgi a cikin teku domin su rage nauyin jirgin. Ana cikin haka, ashe, Yunana ya sauka can ƙarƙashin jirgi ya je ya kwanta, yana ta sharar barcinsa. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki5 Dukan matuƙan jirgin suka firgita, sai kowannensu ya shiga roƙon allahnsa. Suka yi ta jefar da kayan da suke cikin jirgin a ruwa don su sami sauƙi. Yunusa kuwa yana can cikin jirgi, a kwance, yana ta sharar barci. Faic an caibideil |