Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:25 - Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ta haka kuma ashe, Rahab karuwan nan ba a ɗauke ta mai adalci ce saboda abin da ta yi ba ne sa’ad da ta ba wa ’yan leƙen asirin nan masauƙi ta kuma sallame su suka tafi ta wata hanya dabam?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

25 Ashe, ba haka kuma Rahab karuwar nan ta sami kuɓuta saboda aikatawarta ba? Wato, sa'ad da ta sauki jakadun nan, ta fitar da su ta wata hanya dabam?

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:25
15 Iomraidhean Croise  

Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa, Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa, Obed ya haifi Yesse,


“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?” Suka amsa, “Na farin.” Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah.


Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.”


Ta wurin bangaskiya ne ba a kashe Rahab karuwan nan, ta tare da marasa biyayya ba don ta marabci ’yan leƙan asiri.


Amma wani zai ce, “Kai kana da bangaskiya; ni kuma ina da ayyuka.” Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuma zan nuna maka bangaskiyata ta wurin abin da nake yi.


Ai, ka gani cewa bangaskiyarsa da ayyukansa sun yi aiki tare, bangaskiyarsa kuma ta zama cikakkiya ta wurin abin da ya yi.


Kun ga cewa ashe mutum zai sami kuɓuta ta wurin abin da ya yi ne ba ta wurin bangaskiya kaɗai ba.


Sai Yoshuwa ɗan Nun ya aika ’yan leƙen asiri guda biyu a ɓoye daga Shittim ya ce, “Ku je ku duba, ku ga yadda wurin yake, musamman Yeriko.” Sai suka je suka shiga gidan wata karuwa mai suna Rahab, suka sauka a can.


Sai ta zura igiya ta taga suka bi, domin gidan da take yana haɗe da katangar birnin.


Ta ce musu, “Ku tafi cikin tuddan ƙasar don kada mutanen sarki su same ku. Ku ɓuya a can na kwana uku, har sai masu nemanku su komo, sa’an nan ku kama hanyarku.”


Amma matar ta ɓoye mutanen nan biyu. Ta ce, “I, mutanen sun zo wurina, amma ban san daga ina suka zo ba,


(Amma ta kai su saman rufin ɗaki ta ɓoye su a ƙarƙashin karan rama da ta baza a rufin ɗaki.)


Birnin da dukan abin da yake cikinta za a miƙa su ga Ubangiji. Rahab karuwan nan kaɗai ce, da dukan waɗanda suke tare da ita a gidanta za a bari da rai domin ta ɓoye ’yan leƙen asirin ƙasa da muka aika.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan