Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 2:12 - Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ku yi magana ku kuma yi aiki kamar waɗanda za a yi musu shari’a bisa ga doka mai ba da ’yanci,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

12 Saboda haka, maganarku da aikinku su kasance irin na mutanen da za a yi wa shari'a bisa ga ka'idar 'yanci.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 2:12
8 Iomraidhean Croise  

“Ruhun Ubangiji yana kaina, domin ya shafe ni, in yi wa matalauta wa’azin bishara. Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku, in kuma buɗe idanun makafi, in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.


Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”


Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.


A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.


Kuma ko mene ne kuke yi, ko cikin magana ko cikin ayyuka, ku yi shi duka a cikin sunan Ubangiji Yesu, kuna yin godiya ga Allah Uba ta wurinsa.


Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.


In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan