Yahuda 1:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki12 Waɗannan mutane kamar aibobi ne a taronku na soyayya, suna ta shagulgulan ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro, suna kula da kansu kawai. Su kamar holoƙon hadiri ne, wanda iska take korawa. Su kamar itatuwa ne, marasa 'ya'ya da kaka, matattu murus, tumɓukakku. Faic an caibideil |