Rut 1:21 - Sabon Rai Don Kowa 202021 In tafi cikakke, amma Ubangiji ya dawo da ni ba kome. Don me kuke kirana Na’omi? Ubangiji ya wahalshe ni, Maɗaukaki ya kawo mini masifa.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki21 Na tafi a wadace, ga shi, Ubangiji ya komo da ni hannu wofi. Don me kuke kirana mai farin ciki da yake Ubangiji Mai Iko Dukka ya wahalshe ni, ya kuma aukar mini da masifa?” Faic an caibideil |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.