Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Rut 1:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A kwanakin da mahukunta suke mulki an yi yunwa a ƙasar, sai wani mutum daga Betlehem a Yahuda tare da matarsa da ’ya’yansu maza biyu, suka tafi su yi zama na ɗan lokaci a ƙasar Mowab.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

1 A zamanin da mahukunta suke mulkin Isra'ila, aka yi yunwa a ƙasar. Sai wani mutumin Baitalami a Yahudiya ya yi ƙaura zuwa ƙasar Mowab, shi da matarsa, da 'ya'yansa maza biyu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Rut 1:1
26 Iomraidhean Croise  

To, a lokacin, an yi yunwa a ƙasar, sai Abram ya gangara zuwa Masar don yă zauna a can na ɗan lokaci, domin yunwa ta yi tsanani.


Aka yi yunwa a ƙasar; ban da yunwar da aka yi da fari a zamanin Ibrahim, sai Ishaku ya tafi wurin Abimelek sarkin Filistiyawa a Gerar.


A yanzu, yunwa ta yi tsanani a ƙasar.


Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.”


Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab. Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya,


Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.


Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa,


Ya sauko da yunwa a kan ƙasa ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci;


ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.


Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya game da fări cewa,


“Ɗan mutum, in wata ƙasa ta yi mini zunubi ta wurin rashin aminci na kuma miƙa hannuna gāba da ita don in toshe hanyar samun abincinta na kuma aika da yunwa a kanta na kashe mutanenta da dabbobinta,


“Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa balle fa sa’ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi takobi da yunwa da namun jeji da annoba don su kashe mutanenta da dabbobinsu!


Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla.


“Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.


“Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.”


Za ku shuka iri da yawa a gona, amma za ku girbe kaɗan, domin fāra za su cinye su.


Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.


Wani saurayi Balawe daga Betlehem a Yahuda, wanda yake zama cikin zuriyar Yahuda,


ya bar garin ya tafi neman inda zai zauna. A hanyarsa ya zo gidan Mika a ƙasar tudu ta Efraim.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan