Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Obadiya 1:17 - Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Amma a kan Dutsen Sihiyona za a sami ceto; Dutsen zai zama mai tsarki, gidan Yaƙub kuma zai mallaki gādonsa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

17 “Amma za a sami waɗanda za su tsira daga Dutsen Sihiyona, Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki. Jama'ar Yakubu za ta mallaki mallakarta.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Obadiya 1:17
25 Iomraidhean Croise  

gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,


Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya.


A wannan rana Reshen Ubangiji zai zama kyakkyawa da kuma ɗaukaka, kuma amfanin ƙasar zai zama abin fariya da ɗaukakar waɗanda suka rayu a Isra’ila.


Ina kawo adalcina kusa, ba shi da nisa; kuma cetona ba zai jinkirta ba. Zan yi wa Sihiyona ceto, darajata ga Isra’ila.


Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci za su kuma mallaki ƙasar har abada. Su ne reshen da na shuka, aikin hannuwana, don nuna darajata.


Zan fitar da zuriyar Yaƙub, daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna; zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su, a can kuma bayina za su zauna.


Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’


Babu wani daga raguwar Yahuda wanda ya tafi Masar da zai kuɓuta ko ya tsira har ya komo zuwa ƙasar Yahuda, wadda za su yi marmari su komo su zauna; babu wani da zai komo sai dai ’yan gudun hijira.”


Waɗanda suka kuɓuta wa takobi suka komo zuwa ƙasar Yahuda daga Masar za su zama kima kawai. Sa’an nan dukan raguwar Yahuda waɗanda suka zo don su yi zama a Masar za su san maganar wane ne za tă tabbata, tawa ko tasu.


Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub bawana, gama ina tare da kai,” in ji Ubangiji. “Ko da na hallaka dukan al’ummai sarai inda na kora ka, ba zan hallaka ka sarai ba. Zan hore ka amma da adalci kaɗai; ba zan bar ka ba hukunci ba.”


Zan sa mutanena Isra’ila su yi tafiya a kanku. Za su mallake ku, za ku kuma zama gādonsu; ba za ku ƙara sa su rasa ’ya’yansu ba.


Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu, suna kuka kamar kurciyoyin kwaruruka, kowanne saboda zunubansa.


Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’


Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.


“Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.


Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku.


“Tabbatacce idanun Ubangiji Mai Iko Duka suna a kan mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka shi daga fuskar duniya, duk da haka ba zan hallaka gidan Yaƙub ƙaƙaf ba,” in ji Ubangiji.


“Iri zai yi girma da kyau, kuringa za tă ba da ’ya’yanta, ƙasa za tă ba da hatsi, sama kuma za tă ba da raɓa. Zan ba da duk waɗannan abubuwa su zama gādo ga raguwar mutanen nan.


Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.”


Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan