Nehemiya 8:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki9 Nehemiya kuwa wanda yake mai mulki, da Ezra, firist da magatakarda, da Lawiyawa waɗanda suka fassara wa jama'a dokokin, suka ce wa dukan jama'a, “Wannan rana tsattsarka ce, ta Ubangiji Allahnku, kada ku yi baƙin ciki ko kuka.” Gama mutane duka sai kuka suke sa'ad da aka karanta musu dokokin. Faic an caibideil |
Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”