Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 8:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

4 Sai Ezra, magatakarda, ya tsaya a wani dakali na itace, wanda suka shirya musamman domin wannan hidima. Sai Mattitiya, da Shema, da Anaya, da Uriya, da Hilkaya, da Ma'aseya, suka tsaya a wajen damansa, a wajen hagunsa kuwa Fedaiya, da Mishayel, da Malkiya, da Hashum, da Hashbaddana, da Zakariya, da Meshullam suka tsaya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 8:4
16 Iomraidhean Croise  

Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.


Daga zuriyar Bani, akwai Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot.


Daga zuriyar Hashum, akwai Mattenai, da Mattatta, Zabad, Elifelet, Irmai, Manasse, da Shimeyi.


da Hodiya, da Hashum, da Bezai,


da Magfiyash, da Meshullam, da Hezir,


da Rehum, da Hashabna, da Ma’asehiya


da Fashhur, da Amariya, da Malkiya,


da Meshullam, da Abiya, da Miyamin,


da Ma’asehiya ɗan Baruk, ɗan Kol-Hoze, ɗan Hazahiya, ɗan Adahiya, ɗan Yohiyarib, ɗan Zakariya, zuriyar Shela.


Daga zuriyar Benyamin akwai, Sallu ɗan Meshullam, ɗan Yowed, ɗan Fedahiya, ɗan Kolahiya, ɗan Ma’asehiya, ɗan Itiyel, ɗan Yeshahiya,


na iyalin Ezra, Meshullam; na iyalin Amariya, Yehohanan;


Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.


Sai Ezra ya buɗe littafin. Dukan mutane kuwa suka gan shi domin yana tsaye a bisa fiye da inda mutane suke tsaye; yayinda ya buɗe littafin kuwa, dukan mutane suka miƙe tsaye.


Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu.


A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu.


“Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan