Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 10:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Waɗanda suka buga hatimin su ne, Nehemiya ɗan Hakaliya, wanda yake gwamna. Zedekiya

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

1 Waɗanda suka fara sa hannu a takardar alkawarin, su ne mai mulki, wato Nehemiya ɗan Hakaliya, da Zadakiya,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 10:1
11 Iomraidhean Croise  

Sarki ya tsaya dab da ginshiƙi ya kuma sabunta alkawarin a gaban Ubangiji, ya ce zai bi Ubangiji, yă kiyaye dokokinsa, da ƙa’idodinsa, da farillansa, da dukan zuciyarsa da dukan ransa, ta haka ya tabbatar da kalmomin alkawarin da yake a rubuce a cikin littafin nan. Sa’an nan dukan mutane ma suka yi alkawari yin haka.


Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka.


Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.


Kalmomin Nehemiya ɗan Hakaliya. A cikin watan Kisleb a shekara ta ashirin, yayinda nake a fadar Shusha.


da Serahiya, da Azariya, da Irmiya,


“Mun yi alkawari ba za mu ba da ’ya’yanmu mata aure ga mutanen da suke kewaye da mu ba, ba kuwa za mu auri ’ya’yansu mata wa ’ya’yanmu maza ba.


Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim.


Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci.


Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar.


“Saboda wannan duka, muna yin zaunannen alkawari, muna sa shi a rubuce, shugabanninmu kuwa da Lawiyawanmu, da firistocinmu suna buga hatimansu a kai.”


Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan