Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Nehemiya 1:5 - Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Na ce, “Ya Ubangiji Allah na sama, Allah mai girma da mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna da waɗanda suke ƙaunarsa, suke kuma yin biyayya da umarnansa,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

5 Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Nehemiya 1:5
18 Iomraidhean Croise  

ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.


Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?


“Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda.


Sai sarki ya ce mini, “Me kake so?” Sai na yi addu’a ga Allah na sama,


Bayan na dudduba abubuwa, sai na miƙe tsaye na ce wa manyan gari da shugabanni da kuma sauran jama’a, “Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda yake mai girma da banrazana, ku yi yaƙi don ’yan’uwanku, da ’ya’yanku maza da mata, da matanku da kuma gidajenku.”


Dukansu suka ƙulla su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su tā da hankali a cikinta.


“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.


Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!


Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,


Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta.


Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,


Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, wane ne kamar ka? Kai mai iko ne, ya Ubangiji, kuma amincinka ya kewaye ka.


amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.


In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku.


Kada ku tsorata saboda su, gama Ubangiji Allahnku, wanda yake a cikinku, Allah ne mai girma da kuma mai banrazana.


Saboda haka, ku sani cewa Ubangiji Allahnku, shi ne Allah; shi Allah ne mai aminci, yana kiyaye alkawarinsa na ƙauna ga tsararraki dubu na waɗanda suke ƙaunarsa suke kuma kiyaye umarnansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan