M.Sh 7:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 In kuka mai da hankali ga waɗannan dokoki, kuka kuma yi hankali ga bin su, to, Ubangiji Allahnku zai kiyaye alkawarinsa na ƙauna gare ku, kamar yadda ya rantse wa kakanninku. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki12 “Idan za ku saurari waɗannan farillai, ku kiyaye su, sai Ubangiji Allahnku ya cika alkawarin da ya rantse wa kakanninku, ya kuma ƙaunace ku. Faic an caibideil |
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.