Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba.
Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”
Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ”