Ku rubuta dukan waɗannan kalmomin doka a kansu, sa’ad da kuka haye kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji Allah na kakanninku, ya yi muku alkawari.
Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.