Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 4:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 To, ku ji, ya Isra’ila, ku kasa kunne ga ƙa’idodi da dokokin da nake shirin koya muku. Ku bi su domin ku yi tsawon rai, ku kuma shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji, Allahn kakanninku yake ba ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

1 “Yanzu, ya Isra'ilawa, sai ku kiyaye dokoki da farillai da nake koya muku don ku rayu, ku shiga ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allah na kakanninku suke ba ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 4:1
40 Iomraidhean Croise  

don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji.


Ka shimfiɗa farillan da dole a yi biyayya da su.


Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.


Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.


Na ba su ƙa’idodina na kuma sanar musu da dokokina, gama mutumin da ya yi biyayya da su zai rayu ta wurinsu.


“ ‘Amma ’ya’yan suka yi mini tawaye. Ba su bi ƙa’idodina ba, ba su kula su kiyaye dokokina ba, ko da yake mutumin da ya kiyaye su zai rayu ta wurinsu, suka kuma ƙazantar da Asabbataina. Saboda haka na ce zan zuba hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a hamada.


Zan kuma sa Ruhuna a cikinku in kuma motsa ku ku bi ƙa’idodina ku kuma kiyaye dokokina.


“ ‘Bawana Dawuda zai zama sarki a kansu, dukansu kuwa za su kasance da makiyayi guda. Za su bi dokokina su kuma kiyaye ƙa’idodina.


Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji.


“ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.


“ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ”


Ku kiyaye farillaina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.


“Ku kiyaye dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.


kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”


Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.


Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta.


Musa ya bayyana adalcin da yake ga Doka cewa, “Mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu.”


A shekara ta arba’in, a rana ta fari ga wata na goma sha ɗaya, Musa ya yi shela ga Isra’ilawa game da dukan abin da Ubangiji ya umarta shi game da su.


Duba na riga na ba ku wannan ƙasa. Ku shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub, da kuma ga zuriyarsu bayansu.”


To, sai ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kullum ku kuma kiyaye abubuwan da yake bukata, ku kiyaye ƙa’idodinsa, dokokinsa da kuma umarnansu.


ku tabbata kun yi biyayya da dukan ƙa’idodi, da kuma dokokin da nake sawa a gabanku a yau.


In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi,


Gaskiya ce kaɗai za ku bi don ku rayu, ku kuma mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.


Gama na umarce ku a yau, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, don ku yi tafiya a hanyoyinsa, ku kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma dokokinsa, sa’an nan za ku rayu, ku kuma ƙaru, Ubangiji Allahnku kuwa zai albarkace ku a ƙasar da kuke shiga don ci gādonta.


A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da ’ya’yanku ku rayu


don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.


Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.


Waɗannan su ne farillai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Musa ya ba su, sa’ad da suka fito daga Masar.


Wace al’umma ce mai girma haka wadda take da ƙa’idodi da dokoki masu adalci kamar waɗannan ƙunshin dokokin da nake sa a gabanku a yau?


Musa ya tattara dukan Isra’ila ya ce, Ku ji, ya Isra’ila, ƙa’idodi da dokokin da na furta a kunnuwanku a yau. Ku koye su, ku kuma tabbata kun bi su.


Ku yi tafiya cikin dukan hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku, saboda ku zauna, ku yi nasara, ku kuma yi tsawon rai a ƙasar da za ku mallaka.


Waɗannan su ne umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da Ubangiji Allahnku ya umarce ni in koya muku don ku kiyaye a ƙasar da kuke haye Urdun don mallaka,


Ubangiji ya umarce mu mu yi biyayya da dukan waɗannan ƙa’idodi, mu kuma ji tsoron Ubangiji Allahnmu, saboda kullum mu ci gaba, a kuma bar mu da rai, kamar yadda yake a yau.


Saboda haka, sai ku lura, ku bi umarnai, ƙa’idodi, da dokokin nan da nake ba ku a yau.


Ku hankali, ku bi kowane umarnin da nake ba ku a yau, saboda ku rayu, ku ƙaru, ku kuma shiga, ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya alkawarta da rantsuwa ga kakanninku.


Ku yi hankali cewa ba ku manta da Ubangiji Allahnku, har ku kāsa kiyaye umarnansa, dokokinsa da ƙa’idodinsa da nake ba ku a wannan rana ba.


Ku ji, ya Isra’ila. Kuna gab da haye Urdun, ku shiga, ku kuma kori al’ummai da suka fi ku yawa, suka kuma fi ku ƙarfi, masu manyan biranen da suke da katangar da suka yi tsaye zuwa sama.


Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan