9 (Hermon ne Sidoniyawa suke kira Siriyon, Amoriyawa kuwa suna kira shi Senir.)
9 (Sidoniyawa suka kira Harmon, Siriyon, amma Amoriyawa suna ce da shi Senir.)
Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).
Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.
Ya sa dutsen Lebanon ya yi ta tsalle kamar ɗan maraƙi, Siriyon kuma kamar ɗan jakin jeji.
Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.
Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.
Ki tare da ni daga Lebanon, amaryata, zo tare da ni daga Lebanon. Ki gangara daga ƙwanƙolin Amana, daga ƙwanƙolin Senir, ƙwanƙolin Hermon, daga ramin zaki da kuma dutsen da damisoshi suke zama.
Sun yi dukan katakanki daga itatuwan fir daga Senir; sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanon don su yi miki jigon jirgin ruwa.
Daga Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa wajajen Seyir, zuwa Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon ƙasa da Dutsen Hermon. Ya kama sarakunansu ya karkashe su.