M.Sh 27:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Ku rubuta dukan waɗannan kalmomin doka a kansu, sa’ad da kuka haye kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji Allah na kakanninku, ya yi muku alkawari. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki3 Sai ku rubuta kalmomin wannan shari'a a kansu daidai lokacin da kuka haye ku shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasar da take mai yalwar abinci, kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta wa kakanninku. Faic an caibideil |
Isra’ilawa sun yi tafiya a jeji shekaru arba’in, har sai da dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja da suka bar Masar suka mutu, domin ba su yi wa Ubangiji biyayya ba. Gama Ubangiji ya rantse cewa ba zai bar su su ga ƙasar da ya yi wa iyayensu alkawari da rantsuwa cewa zai ba su ba, ƙasar da zuma da madara suke kwarara, ƙasar da take cike da albarka.