M.Sh 20:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki1 “Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku. Faic an caibideil |
Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”