Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 2:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Ka ba wa mutane waɗannan umarnai, ka ce, ‘Kuna gab da wucewa cikin yankin ’yan’uwanku, zuriyar Isuwa, wanda yake zama a Seyir. Za su ji tsoronku, amma ku yi hankali

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

4 Ka umarci jama'a, su bi yankin ƙasar zuriyar Isuwa, danginku, waɗanda suke zaune a Seyir. Za su ji tsoronku, sai ku yi hankali,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 2:4
15 Iomraidhean Croise  

Ubangiji ya ce mata, “Al’ummai biyu suna a cikin mahaifarki mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin.”


Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.


Sarakunan Edom za su tsorata, shugabannin Mowab za su yi rawar jiki, mutanen Kan’ana za su narke.


Razana da tsoro za su fāɗo a kansu. Da ikon hannunka za su tsaya cik kamar dutse, har sai mutanen da ka kawo sun wuce, ya Ubangiji.


Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.


Sai ya ce musu, “Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”


Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.


“Kun yi ta yawo kewaye da ƙasar tudun nan da daɗewa; yanzu ku juya, ku nufi arewa.


Kada ku yi ƙyamar mutumin Edom, gama mutumin Edom ɗan’uwanku ne. Kada ku yi ƙyamar mutumin Masar, domin kun yi zama baƙunta a ƙasarsa.


don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya


Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan