Ba su yi nisa da birnin ba sa’ad da Yusuf ya ce wa mai yin masa hidima, “Tashi, ka bi waɗannan mutane nan da nan, in ka same su, ka ce musu, ‘Me ya sa kuka sāka alheri da mugunta?
Dukan shekarun da muka yi a tafiyarmu daga Kadesh Barneya zuwa lokacin da muka ƙetare Kwarin Zered, sun kai shekaru talatin da takwas. A lokacin, wannan tsara gaba ɗaya ta mutanen da suka isa yaƙi sun mutu daga sansani, yadda Ubangiji ya rantse musu.
Dalilin da ya sa ya yi haka shi ne, dukan waɗanda suka fito daga Masar, dukan mazan da suka kai shekarun shiga soja, sun mutu a cikin jeji a hanya bayan sun bar Masar.