M.Sh 13:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki3 kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku. Faic an caibideil |
To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’