Ubangiji kuma zai bugi Isra’ila, har tă zama kamar kyauro mai girgiza a bakin rafi. Zai tumɓuke Isra’ila daga wannan ƙasa mai kyau da ya ba wa kakanninsu, yă watsar da su gaba da Kogin Yuferites domin sun tsokane Ubangiji har ya yi fushi, ta wurin yin ginshiƙan Ashera.
Ku rurrushe bagadansu, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu, ku kuma ƙone ginshiƙan Asheransu da wuta; ku yayyanka gumakan allolinsu, ku kuma shafe sunayensu daga waɗannan wurare.
Amma sai ku nemi wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa daga cikin dukan kabilanku, inda zai sa Sunansa, yă mai wurin mazauninsa. A wannan wuri ne za ku tafi;