Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




M.Sh 1:42 - Sabon Rai Don Kowa 2020

42 Amma Ubangiji ya ce mini, “In faɗa muku, ‘Kada ku fāɗa musu da yaƙi, gama ba zai kasance tare da ku ba. Idan kuka kuskura, abokan gābanku za su murƙushe ku.’ ”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

42 “Amma Ubangiji ya ce mini in faɗa muku, kada ku tafi kada kuma ku yi yaƙi, gama ba ya tare da ku. Maƙiyanku za su kore ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




M.Sh 1:42
8 Iomraidhean Croise  

Dubu za su gudu don barazanar mutum guda; da jin barazanar mutane biyar dukanku za ku yi ta gudu sai an bar ku kamar sandar tuta a kan dutse, kamar tuta a kan tudu.”


Ko da sun yi renon ’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya!


Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba.


Saboda haka Filistiyawa suka yi yaƙi, Isra’ilawa kuwa suka sha ɗibga, kowane mutum kuwa ya gudu zuwa tentinsa. Kisan kuwa ya yi muni ƙwarai. Isra’ilawa sun rasa mayaƙa dubu talatin.


Filistiyawa suka tunƙuro mayaƙansu domin su sadu da Isra’ilawa, yaƙi kuwa ya yi tsanani har Isra’ilawa suka sha kashi a hannun Filistiyawa. Filistiyawa suka kashe Isra’ilawa kusan mutum dubu huɗu a bakin dāgā.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan