Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mika 3:3 - Sabon Rai Don Kowa 2020

3 ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

3 Kuna cin naman mutanena, kuna feɗe fatar jikinsu, Kuna kakkarya ƙasusuwansu, Kuna yanyanka su gunduwa gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mika 3:3
11 Iomraidhean Croise  

Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?


Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi.


waɗanda haƙoransu takuba ne waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne don su cinye matalauta daga duniya da kuma mabukata daga cikin mutane.


Ubangiji yana shari’a da dattawa da kuma shugabannin mutanensa, “Ku ne kuka lalace gonar inabina; ganimar talakawa suna a gidajenku.


Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena kuna gurgurje fuskokin talakawa?” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.


Suna cewa, ‘Lokaci bai yi kusa da za a gina gidaje ba? Wannan birni yana tukunyar dahuwa, mu ne kuwa naman.’


Ka sa gunduwoyin nama a cikinta dukan gunduwoyi masu kyau, cinya da kafaɗa. Ka cika ta da waɗannan ƙasusuwa mafi kyau;


Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata kuka kori matalautan ƙasar.


Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar magabci. Kun tuɓe riga mai tsada daga waɗanda suke wucewa ba tare da kun damu ba, sai ka ce mutanen da suke komowa daga yaƙi.


Sarakunanki ruri ne na zakoki, shugabanninki kyarketan dare ne, waɗanda ba sa rage kome don safe.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan