Mika 1:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki2 Dukanku ku ji, ku al'ummai! Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan abin da yake cikinki. Bari Ubangiji Allah Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama shaida a kanku. Faic an caibideil |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.