Mattiyu 7:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki17 Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan 'ya'ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan 'ya'ya. Faic an caibideil |
Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.