Mattiyu 7:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki12 Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.” Faic an caibideil |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.