suka kawo wa Dawuda da mutanensa tabarmai, da kwanoni, da kayayyakin da aka yi da yumɓu. Suka kuma kawo alkama da sha’ir, da gari, da soyayyen hatsi, da wake, da waken barewa,
Mai adalci yakan mutu, ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa; an kwashe mutanen kirki, ba kuwa wanda ya fahimta cewa an kwashe masu adalci don a tsame su daga mugunta.
Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”
Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama, gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu.
Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ”
Ya nuna maka, ya mutum, abin da yake mai kyau. Me Ubangiji yake bukata daga gare ka kuwa shi ne ka yi gaskiya ka so aikata jinƙai ka kuma yi tafiya da tawali’u a gaban Allah.
A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”
Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.
Ko da yake a dā ni mai saɓo da mai tsanantawa da kuma mai rikici ne, aka nuna mini jinƙai saboda na yi haka cikin jahilci ne da kuma rashin bangaskiya.
Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.
Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.
Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma.