Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 5:44 - Sabon Rai Don Kowa 2020

44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

44 Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu'a,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 5:44
21 Iomraidhean Croise  

Elisha ya ce, “Kada ka kashe su. Za ka kashe mutanen da ka kame da takobi ko bakanka? Ka ba su abinci da ruwa su ci, su sha, sa’an nan su koma wurin maigidansu.”


in na yi mugunta ga wanda yake zaman lafiya da ni ko kuwa ba da wani dalilin cuci abokin gābana,


Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.


Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.


“Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.


Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!”


Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.


Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.


Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.


Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci.


Kada ku rama mugunta da mugunta ko zagi da zagi, sai dai ku sa albarka, gama ga wannan ne aka kira ku, ku kuma gāji albarka.


Ya ce, “Ka fi ni gaskiya, ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan