43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan'uwanka, ka ƙi magabcinka.’
Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu.
“ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”
“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’
“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’
Ba mutumin Ammon, ko mutumin Mowab, ko kuwa wani zuriyarsu da zai shiga taron jama’ar Ubangiji, har tsara ta goma.
Kada ku yi yarjejjeniyar abuta da su, muddin kuna da rai.
Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, sa’ad da kuka fito Masar.
In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.
Ya kuma ba mu wannan umarni cewa duk wanda yake ƙaunar Allah, dole yă ƙaunaci ɗan’uwansa.