Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, “Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”
don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya
Asirin taurari bakwai da ka gani a hannuna na dama da kuma na alkukan fitilu bakwai na zinariya shi ne, Taurarin bakwai ɗin nan, mala’ikun ikkilisiyoyi bakwai ne; alkukan fitilu bakwai ɗin nan kuma ikkilisiyoyi bakwai ne.
Ka tuna da matsayinka a dā kafin ka fāɗi! Ka tuba ka kuma yi ayyukan da ka yi da fari. In ba ka tuba ba, zan zo wajenka in ɗauke wurin ajiye fitilanka daga inda yake.