Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi.
Suka ce, “Duba, mu bayinka muna da masu ji da ƙarfi hamsin. Bari su je su nemi maigidanka. Wataƙila, Ruhun Ubangiji ya ɗauke shi ya ajiye bisa wani dutse, ko wani kwari.” Elisha ya ce, “A’a, kada ku aike su.”
Sa’an nan Ruhu ya ɗaga ni sama ya kawo ni ƙofar gidan Ubangiji wadda take fuskantar gabas. Can a mashigi zuwa ƙofar akwai mutum ashirin da biyar, na kuma ga a cikinsu akwai Ya’azaniya ɗan Azzur da Felatiya ɗan Benahiya, shugabannin jama’a.
Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma kawo ni ga masu zaman bauta a ƙasar Babilon cikin wahayin da Ruhun Allah ya bayar. Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni,
Cikin wahayin, Allah ya kai ni ƙasar Isra’ila ya sa ni a kan wani dutse mai tsayi ƙwarai, inda a gefen kudunsa akwai gine-ginen da suka yi kamar birni.
Ya miƙa abin da ya yi kamar hannu ya kama a gashin kaina. Ruhu ya ɗaga ni tsakanin sama da ƙasa, a cikin wahayoyi kuma Allah ya ɗauke ni zuwa Urushalima, zuwa ƙofa zuwa gabas na cikin fili, inda gunki mai tsokanar kishi yake tsaye.
Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.