Yanzu sai ku gyara hanyoyinku da kuma ayyukanku ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku. Sa’an nan Ubangiji zai yi juyayi ya kuma janye masifar da ya furta zai kawo a kanku.
Wataƙila sa’ad da mutanen Yahuda suka ji game da kowace masifar da na shirya in auka musu, kowa ya juya daga muguwar hanyarsa; sa’an nan in gafarta musu muguntarsu da kuma zunubinsu.”
Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.
Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu.