Waɗannan sanduna sun yi tsawo ƙwarai har ƙarshensu sun nausa daga akwatin alkawarin, ana iya ganinsu daga gaban ciki wuri mai tsarki na can ciki amma ba daga waje Wuri Mai Tsarki ba; kuma suna nan a can har wa yau.
Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau.