Mattiyu 27:29 - Sabon Rai Don Kowa 202029 Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki29 Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!” Faic an caibideil |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”