Mattiyu 26:61 - Sabon Rai Don Kowa 202061 suka furta cewa, “Wannan mutum ya ce, ‘Ina iya rushe haikalin Allah, in sāke gina shi cikin kwana uku.’ ” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki61 suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.” Faic an caibideil |
Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansa da kuma Mai Tsarkin nan na Isra’ila gare shi wanda al’ummai suka rena suka kuma ki, ga bawan masu mulki. “Sarakuna za su gan ka su kuma miƙe tsaye, sarakuna za su gani su kuma rusuna, saboda Ubangiji, wanda yake mai aminci, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, wanda ya zaɓe ka.”
Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.