Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Mattiyu 26:42 - Sabon Rai Don Kowa 2020

42 Ya sāke tafiya sau na biyu, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in ba zai yiwu a ɗauke wannan kwaf ba sai na sha shi, to, bari a aikata nufinka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

42 Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Mattiyu 26:42
14 Iomraidhean Croise  

Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?” Suka amsa, “Za mu iya.”


Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, “Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”


Da ya dawo, har yanzu ya tarar suna barci, domin idanunsu sun yi nauyi da barci.


mulkinka yă zo a aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a sama.


Ya ce, “Ya Abba, Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”


“Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.”


Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.


Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan