20 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun.
20 Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu.
Ga yadda za ku ci shi, ku yi ɗamara, takalma kuwa a ƙafafunku, kuna riƙe da sandunan tafiya a hannunku. Ku ci shi da gaggawa; Bikin Ƙetarewa ne na Ubangiji.
Yayinda sarki yake a teburinsa, turarena ya bazu da ƙanshi.
Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.
Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”