Gama kowace rana suna nemana; suna marmarin sanin hanyoyina, sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba. Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su.
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Sardis, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi, na wanda yake riƙe da ruhohi bakwai na Allah da kuma taurari bakwai. Na san ayyukanka; ana ganinka kamar rayayye, amma kai matacce ne.