Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”
“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.
Ta wurin bangaskiya Nuhu, sa’ad da aka yi masa gargaɗi a kan abubuwan da ba a gani ba tukuna, a cikin tsoro mai tsarki ya sassaƙa jirgi don ceton iyalinsa. Ta wurin bangaskiyarsa ya hukunta duniya ya kuma zama magājin adalcin da ake samu ta wurin bangaskiya.
in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai;