Za a tumɓuke dukan taurarin sammai za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi; dukan rundunar sama za su fāffāɗi kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa, kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure.
Ku daga idanunku zuwa sammai ku dubi duniya a ƙasa; sammai za su ɓace kamar hayaƙi, duniya za tă shuɗe kamar riga mazaunanta kuma su mutu kamar ƙudaje. Amma cetona zai dawwama har abada, adalcina ba zai taɓa kāsa ba.
Ko da duwatsu za su girgiza a kuma tumɓuke tuddai, duk da haka madawwamiyar ƙaunata da nake yi miki ba za tă jijjigu ba ba kuwa za a kawar da alkawarin salamata ba,” in ji Ubangiji, wanda ya ji tausayinki.
Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Lawodiseya, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomina Amin, amintaccen mashaidi mai gaskiya, da kuma mai mulkin halittar Allah.