20 Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.
20 Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar.
Ku lura fa, ai, Ubangiji ne ya ba ku Asabbaci; shi ya sa a kan ba ku burodi na kwana biyu, a rana ta shida. Kowa ya kamata yă kasance inda yake a rana ta bakwai; kada kowa yă fita.”
Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!
Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.
Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin.